Mene ne Bitcoin? Hanyoyi huɗu da za su taimaka muku wajen fahimtar kuɗin Intanet – BBC News Hausa
Batun kuɗin intanet na Bitcoin ya sake dawowa a tsakanin jama’a. Masu kutse na neman ha’intar jama’a a shafukan Tuwita da sauran shafukan sada zumunta, inda suke neman mutane su aika musu nau’in kuɗin ta hanyar amfani da shafukan manyan mutane.